Home Home ‘Yan Sandan Najeriya Za Su Yi Nazari Kan Gargaɗin Amurka

‘Yan Sandan Najeriya Za Su Yi Nazari Kan Gargaɗin Amurka

172
0
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce za ta yi nazari a kan gargaɗin da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar, inda ya yi gargaɗi a kan yiwuwar kai hare-hare a Nijeriya, musamman a birnin Abuja.

A wata sanarwa da ta fitar kwana ɗaya bayan gargadin na Amurkan da Birtaniya, hukumar ‘yan sandan ta ce yin nazarin ya zama wajibi, saboda kasancewar rundunar ce a kan gaba wajen tabbatar da tsaro na cikin gida.

Ta ce ba za su yi biris da bayanan leƙen asiri a kan barazanar tsaro ba, duk da cewa babu wani abu na tashin hankali da ke faruwa kuma a shirye su ke su yi duk abin da ya dace domin shawo kan duk wata barazana.

Rundunar ‘yan sandan, ta ce shugaban ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba, ya bada umarnin dukkan kwamishinonin ‘yan sanda na jihohi su kasance cikin shiri, tare da sake dabarun samar da tsaro ga al’umma.

Leave a Reply