Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Sandan Jihohi: Kawunan Gwamnonin Nijeriya Sun Rabu

Kayode Fayemi, Gwamna Jihar Ekiti

Kayode Fayemi, Gwamna Jihar Ekiti

Kawunan Gwamnonin jihohin Nijeriya 36, sun rarrabu a kan batun fito da ‘yan sandan jiha da na kananan hukumomi yayin da su ke ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya shaida wa manema labarai cewa, an kasa maganar kirkirar ‘yan sandan jihohi a faifai, amma ba a samu matsaya guda daga wajen gwamnoni ba.

Wannan kuwa ya kasance ne, saboda karfin jihohin ba daya ne ba, yayin da wasu jihohin ke da kudin da za su iya gudanar da lamarin sauran ba su da shi.

Kudurin kirkirar ‘yan sandan jiha dai ya na daga cikin kudurorin kwamitin da shugaban kasa ya kafa a kan binciken keta hakkin dan Adam da dakarun SARS ke yi, ya kuma kammala binciken tare da mika rahoton shi ga shugaba Buhari a makon da ya gabata.

Exit mobile version