Home Labarai ‘Yan Sandan Jihar Ribas Sun Kama Sija Huɗu

‘Yan Sandan Jihar Ribas Sun Kama Sija Huɗu

118
0
Nigeria Police Force (3)
Nigeria Police Force (3)

Rundunar ‘yansandan reshen jihar Ribas ta kama mutum 13 da take zargi da fashi da kuma satar kayan abinci.


Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ta fitar ranar Litinin ta ce cikin waɗanda ake zargin akwai soja huɗu,

da jami’in rundunar tsaro ta Civil Defence. Grace Iringe-Koko ta ce sun yi nasarar kama mutanen ne


sakamakon wani bincike bayan kama wani da ake zargi da haura gidan ajiyar abinci a ƙaramar hukumar
Ohio/Akpor ta jihar.


Ta ce biyu daga cikin mutanen farko da aka kama kofur-kofur ne a rundunar sojin Najeriya da ke aiki a jihar Delta,

da kuma jami’i a rundunar tsaro ta Civil Defence mai aiki a Kabba da ke jihar Kogi.


Ta ƙara da cewa daga baya ne suka gano wani babban gungu na masu aikata fashi da kuma karkatar da kayayyakin mutane,

ciki har da manyan motoci. A cewar ta, rundunar ta ƙwace mota ƙirar Toyota Hilux da gungun mutanen ke amfani da ita.

Leave a Reply