Home Labarai Yan Sandan Duniya Sun Hadu Domin Dakile Ayyukan Kungiyar Matsafa Ta Black...

Yan Sandan Duniya Sun Hadu Domin Dakile Ayyukan Kungiyar Matsafa Ta Black Axe

221
0
black axe logo design template free vector
black axe logo design template free vector

Ƴansanda a faɗin duniya sun haɗa hannu inda suka gudanar da wani samame domin daƙile ayyukan ɗaya daga cikin ƙungiyoyin masu aikata laifuka mafiya hatsari – wato Black Axe.

A lokacin gagarumin samamen da ƴansandan suka aiwatar wanda aka yi wa laƙabi da Operation Jackal III, jami’ai sun kai samame a ƙasashe 21 tsakanin watan Afrilu zuwa Yulin 2024.

Samamen wanda rundunar ƴansanda ta duniya ‘Interpol’ ta aiwatar, ya samu nasarar kama mutum 300 waɗanda ke da alaƙa da ƙungiyar ta Black Axe da wasu ƙungiyoyi masu alaƙa da ita.

Hukumar ƴansandan duniya ta Interpol ta bayyana lamarin a matsayin wata ‘babbar illa’ ga gungun masu aikata miyagun lafiuka na Najeriya,

sai dai hukumar ta yi gargaɗin cewa har yanzu ƙungiyar na da matuƙar haɗari idan aka yi la’akari da yawan ƴan ƙungiyar a faɗin duniya da kuma ƙarfin da take da shi.

A ɗaya daga cikin irin wannan samame, hukumomi a Canada sun ce sun bankaɗo wani tsarin damfara mai alaƙa da ƙungiyar Black Axe na kuɗi sama da dala biliyan biyar (£3.8bn) a shekarar 2017.

Leave a Reply