Home Home ‘Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Dabar Da Ke Amfani Da Wuƙaƙe Don...

‘Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Dabar Da Ke Amfani Da Wuƙaƙe Don Cutar Da Mutane A Kano

1
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, ta kama wasu da ake zargi da aikata dabanci ta hanyar amfani da wuƙaƙe su na gallaza wa mutane a birnin Kano.

Bayanai daga wajen waɗanda ayyukan ‘yan dabar ya shafa sun ce, mutanen da ake tuhuma su kan yi amfani da tituna masu cunkoso da wuraren taron jama’a domin aikata ta’asar.

Rahotanni sun ce, ayyukan ‘yan dabar sun yi sanadiyyar mutuwar mutane, yayin da waɗanda su ka samu tsira kuma ke gamuwa da munanan raunuka.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi kira ga jama’a su taimaka wa rundunar wajen gano sauran ‘yan ƙungiyar da ke cikin ƙwaryar birnin.