Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Sanda Sun Kama Madugun Masu Garkuwa Da Mutane A Jalingo

Dakarun ‘yan sanda na musamman da ke karkashin kulawar shugaban ‘yan sandan sun samu nasarar kama wani madugun masu garkuwa da mutane a jihar Taraba mai suna Fuski Angulu.

Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun ruwaito cewa, Fuski Angulu shine ummul haba’isun karuwar hare haren yan bindiga tare da satar mutane da nufin yin garkuwa dasu da kuma fashi da makami a Takum, Donga da garin Wukari.

Jaridar ta kara da cewa, yan sandan sun samu bayanan sirri ne a kan madugun masu garkuwa da mutanan, wanfda hakan y aba su damar kai mashi samame su ka kuma samu nasarar yi awon gaba dashi zuwa Abuja.

Sai dai da ya ke amsa tambayoyi, Fuski ya fallasa sunan daya daga cikin makarraban sa mai suna Idi Shaidan wanda ke zaune a garin Jalingo da ke jihar Taraba.

Haka kuma ya ambaci sunan wani tsohon mai ba gwamnan jihar Taraba shawara a kan muradun karni mai suna Salejo Damburan, da kuma wani kansila a karamar hukumar Jalingo  Shagari Umar a matsayin wadanda ke daukar nauyin sa.

Dajin haka sai jami’an ‘yan sandan suka dira jihar Taraba su ka kuma  awon gaba da Damburam, Shagari da kuma wani Sunday Kona, sannan suka gudanar da binciken kwakwaf a gidajen su.

Sai dai Danburam ya musanta zargin cewa yana da hannu cikin miyagun ayyukan, amma ya bayyana cewa ya na sane da cewa Idi Shaidan na daga cikin wadanda suke addabar gidan sa da kamfanin sa a Jalingo, domin kuwa ya taba kai karar sa ga shugaban hukumar DSS na jihar Taraba da kuma jami’an ‘yan sanda na SARS.

Exit mobile version