Home Labaru Yan Sanda Sun Hana Ɓangaren Ibrahim Shekarau Gudanar Da Zaɓe

Yan Sanda Sun Hana Ɓangaren Ibrahim Shekarau Gudanar Da Zaɓe

15
0

Bangaren jam’iyyar APC da ke adawa da salon shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano bai samu damar gudanar da zaɓen shugabancin jam’iyyar ba yayin da ɓangaren gwamnati ke aiwatar da na sa.

Ɓangaren wanda tsohon Gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau da wasu ‘yan majalisar tarayya ke jagoranta ya shirya gudanar da zaɓen ne a cibiyar matasa ta Sani Abacha dake Kano, sai dai ‘yan sanda sun hana kowa shiga wurin taron, kamar yadda wakilin BBC a Kano Khalifa Dokaji ya bayyana.

A halin da ake ciki dai Jagororin taron sun bayyana cewa za su sanar da wata ranar da za su gudanar da zaɓen.

A gefe guda kuma, ɓangaren Gwamna Umar Ganduje ya gudanar da zaɓen ne a rufaffen filin wasa na Sani Abacha, kuma gwamnan ya ce su ne kaɗai shugabancin jam’iyyar na ƙasa ya amince su yi zaɓen a yau Asabar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ƙara da cewa za su nemi ɗaya ɓangaren domin tattaunawa.