Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

’Yan Sanda Sun Gano Masu Yunkurin Tada Fitina Zaben Jihar Filato

An naɗa sabon Sarkin Sudan na Kontagora a jihar Neja, kwanaki bayan rasuwar sarkin masarautar.

Kwamishinan ƙananan hukumomi da Masarautun Gargajiya Emmanuel Umar ne ya sanar da nadin Mohammed Barau a matsayin sabon Sarkin ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce an zaɓi sabon Sarkin Sudan na Kontagoran ne a ranar Lahadi 19 ga watan Satumban 2021, kuma manyan masu zaɓar sarki na masarautar ne suka yi hakan.

Kwamishinan ya ce: “Masu zabar sarkin sun tabbatar wa gwamna cewa sun yi zaɓen ne ta hanyar bin dokoki da al’adun Masarautar Kontagora, kuma sun yanke hukuncin ne bisa fahimtarsu ba tare da tsoma bakin wani daga waje ba.

Sanarwar ta ce kamar yadda doka ta tanadar gwamna, ya amince da matakin nasu tare da tabbatar da Mohammed Barau Kontagora a matsayin Sarkin Sudan na bakwai.

Exit mobile version