Home Labarai ‘‘Yan Sanda Sun Ƙaryata Shigowar Wata Baƙuwar Halitta Cikin Katsina

‘‘Yan Sanda Sun Ƙaryata Shigowar Wata Baƙuwar Halitta Cikin Katsina

3
0

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina, ta ƙaryata wani faifan
bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo,
wanda ke nuna yadda wata baƙuwar halitta da ba a san ko
wacce iri ce ba ta shiga jihar.

A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar SP Gambo Isah ya fitar, ya ce an janyo hankalin rundunar ‘yan sanda ta jihar a kan wani faifan bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna yadda wasu baƙin halittu su ka mamaye Katsina.

Sanarwar ta cigaba da cewa, Hukumar ta na so ta bayyana cewa abubuwan da ke cikin bidiyon gaba ɗaya ƙarya ne, wani yunƙuri ne kawai domin a kawo cikas ga zaman lafiyar da mutanen jihar ke amfana da shi.

Kakakin rundunar SP Gambo Isah, ya buƙaci jama’a da cewa kada su firgita, su yi watsi da faifan bidiyon na bogi da abubuwan da ke cikin sa.