Home Labaru Kiwon Lafiya ‘Yan Nijeriya Miliyan 10 Na Zukar Tabar Wiwi

‘Yan Nijeriya Miliyan 10 Na Zukar Tabar Wiwi

1088
0

Kungiyar sa-ido a kan safara da shan miyagun kwayoyi da manyan laifuffuka ta majalisar dinkin duniya, ta ce akalla mutane miliyan 10 ke tu’ammali da ganyen tabar wiwi a Nijeriya.

Kungiyar ta bayyana haka ne, a wajen taron samun madafa game da illar amfani da miyagun kwayoyi da aka yi a Abuja.

Haka kuma, kjungiyar ta ce shan ganyen tabar Wiwi ya zama ruwan dare, domin akalla mutane miliyan 188 ke amfani da ita a fadin duniya.

Jami’in kungiyar Oliver Stolpe ya bayyana cewa, kungiyar su ta gano haka ne a wani bincike da ta yi a shekara ta 2018.

Leave a Reply