‘Yan Nijeriya na ci-gaba da bayyana damuwa a kan yadda
shugaba Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni ke ci-gaba
da nada mukamai tare da bada kwangiloli a daidai lokacin da
su ke gab da sauka daga karagar mulki.
Yayin da wasu ke kallon matakin a matsayin wani tarko da gwamnatin ke dana ma wadanda za su gaje su, zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnoni masu jiran gado sun ki cewa uffan a bainar jama’a dangane da wadannan mataki.
Rahotanni daga matakin tarayya zuwa jihohi na nuna yadda shugaba Buhari ke ci-gaba da nade-nade, da kuma amincewa da sabbin kwangiloli na miliyoyin naira, yayin da gwamnonin jihohi ke bin irin wannan mataki, wanda ke samun goyon baya ko amincewar majalisar kasa da ta jihohi.
Daga cikin irin wadannan bukatu dai har da amincewa a ciwo bashin dala miliyan 800 daga Bankin Duniya da majalisar kasa ta yi, domin raba wa talakawa a matsayin rage radadin cire tallafin mai da gwamnati ta dakatar da aiwatarwa, da kuma gabatar da bukatar biyan dala miliyan 556 da Fan miliyan 98 da naira miliyan 226 a matsayin basussukan shari’ar da ake bin gwamnatin tarayya.