Home Labaru Kiwon Lafiya ‘Yan Najeriya Miliyan 71 Na Fama Da Bakin Talauci – Rahoto

‘Yan Najeriya Miliyan 71 Na Fama Da Bakin Talauci – Rahoto

103
0

Wata sabuwar kididdiga ta duniya ta bayyana cewa, kimanin
‘yan Nijeriya miliyan 71 su na fama da bakin talauci, yayin da
aka bayyana jihar Yobe a matsayin wadda ta fi fama da
yunwa a Nijeriya.

Dan takarar gwamnan jihar Rivers a karkashin jam’iyyar APC Tonye Cole da ya gabatar da makala a wani taron ranar tunawa da yaki da yunwa ta duniya a Abuja, ya ce wasu alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun ce, mutane dubu 25 ne ke mutuwa a kowace rana sakamakon yunwa, wadanda su ka hada da kananan yara dubu 10 a duniya.

Mista Cole ya kara da cewa, Hukumar Kididdiga ta kasa ta kiyasta mutane miliyan 133 da ke fama da nau’uka daban- daban na yunwa a Nijeriya.

Ya ce, ya zama dole Nijeriya ta dauki mataki domin tunkarar wannan matsala ta bakin talauci a fadin Nijeriya.

Leave a Reply