Home Labaru ‘Yan Mata Bakwai Sun Rasu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Jihar Jigawa

‘Yan Mata Bakwai Sun Rasu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Jihar Jigawa

332
0

Rahotanni daga Jihar Jigawa na cewa wasu ‘yan mata bakwai sun rasa rayukan su bayan kwale-kwalen da su ke tafiya a ciki ya kife a ranar Alhamis da ta gabata da dare.

Lamarin dai ya faru ne, yayin da su ke kokarin tsallaka wani kogi a kan hanyar su ta dawowa daga taron Maulidi a garin Gasanya.

Bayanai sun ce jirgin ya na dauke da mutane 12 ne, lokacin da ya kife cikin kogin da ke tsakanin kananan hukumomin Auyo da Kafin Hausa.

Daya daga cikin iyayen yaran da su ka rasu Malam Mikail Jibril, ya ce shekarun ‘yan matan ba su wuce 11 ba zuwa 12 ba, yayin da Mai garin Gafasa Alhaji Adamu Abdullahi ya ce tuni an yi jana’izar su.

Leave a Reply