Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Majalisa Za Su Koma Hutun Domin Yi Wa Kasafin 2020 Kwaskwarima

Kasafin 2020: ‘Yan Majalisa Za Su Koma Hutun Domin Yi Wa Kasafin 2020 Kwaskwarima

Kasafin 2020: ‘Yan Majalisa Za Su Koma Hutun Domin Yi Wa Kasafin 2020 Kwaskwarima

‘Yan majalisun dokokin tarayya sun katse hutun Sallar domin komawa bakin aiki cikin gaggawa, saboda yin nazari ga daftarin kwaskwararren kasafin kudin shekara ta 2020.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin akawun majalisar, Muhammad Sani Omolori a wata sanarwa da ya fitar, tare da cewa ‘yan majalisar za su koma aiki ne a ranar Alhamis 28 ga watan Mayu.

Omolori ya kara da cewa, ana sanar da sanatoci da ‘yan majalisar wakilai da cewa, an sauya ranar komawa majalisa daga Talata 2 ga watan yuni zuwa Alhamis 28 ga watan Mayun 2020.

Akawun majalisar ya cigaba da cewa, an yi haka ne domin ba ‘yan majalisar damar yin nazari ga daftarin kwaskwararren kasafin kudin shekara ta 2020, saboda haka akew bukatar Sanatoci da yan majalisar wakilai su hallarci majalisa da karfe 10 na safiyar Alhamis 28 ga watan Mayu.

Tun farko dai, shugaban majalisar dattawa sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa, akwai yiwuwar su koma aiki kafin karewar hutun da zarar sun samu sakon daga bangaren zartarwa game da kasafin kudin 2020.

Exit mobile version