‘Yan majalisar dattawa sun ce za su fara hutu a cikin wannan watan, muddin shugaba Muhammadu Buhari bai gabatar ma su da sunayen wadanda ya ke son nadawa a matsayin Ministocin sa ba.
Wata majiya ta ce sanatocin ba za su fasa zuwa hutu idan lokaci ya yi ba, saboda kawai su na jiran shugaban kasa ya aika da sunayen Ministocin da a ke jira tun bayan da APC ta yi nasara a zaben shekara ta 2019 ba.
Karanta Labarun Masu Alaka: Ana Zaton Ambode Da Bindo Za Su Samu Mukamin Minista
Majiyar ta ce, wasu daga cikin Sanatocin sun nuna rashin jin dadi bisa jinkirin da shugaba Buhari key i na gabatar da sunayen ba.
Sanatoci sun nuna cewa, rashin gabatar da sunayen Ministocin ba zai sa su fasa zuwa hutu a Ranar 26 ga Watan Yuli ba.
Karanta Labarun Masu Alaka: Tarayyar Turai Za Ta Mika Rahoton Ta Ga Majalisar Dattawa
Sanata Adedayo Adeyeye, ya ce zai yi kyau shugaba Buhari ya aika masu sunayen Ministocin sa a tantance su kafin su tafi dogon hutu, saboda a samu gwamnati ta soma aiki gadan-gadan.