‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya sun sadaukar da rabin albashinsu domin tallafa wa yaki da cutar coronavirus.
Kakakin Majalisar, Sanata Godiya Akwashiki ya sanar da cewa daga watan Maris da muke ciki ‘yan Majalisar za su ci gaba da bayar da bayar da rabin albashinsu har sai an magance cutar a Najeriya.
Sanarwar gudunmuwar sanatocin na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan ministocin kasar sun sanar da mika da rabin albashinsu na watan Maris a matsayin tallafi ga kokarin kasar na yaki da annobar.
Tallafin nasu kadan ne daga irin taimakon da gwamantin kasar ta samu daga kamfanoni da attajirai da shugabani a yakin da ta ke yi da COVID-19.