Home Labaru ‘Yan Damfara Na Karɓar Bashin Banki Da Lambar Wayar ’Yan Sanda

‘Yan Damfara Na Karɓar Bashin Banki Da Lambar Wayar ’Yan Sanda

126
0

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun,
ya gargaɗi ‘yan Nijeriya su daina amfani da lambobin
gaugawa na ’yan sanda wajen karɓar bashi daga bankuna da
sauran kamfanonin bada bashi.

Egbetokun ya yi gargaɗin ne, a cikin wata sanarwa da kwamishinan ‘yan sanda na birnin tarayya Abuja CP Haruna G. Garba ya fitar, inda ya ce wasu mutane su na amfani da layukan gaugawa su na cin bashin kamfanonin bada bashi da ruwa.

Ya ce kwamishinan ya umurci mutanen da ke shigar da layukan gaugawa na ‘yan sanda a cikin mugayen ayyukan su, da nufin yaudarar jama’a da waɗanda su ka miƙa kai don samun lamuni su ƙaurace wa irin waɗannan ayyuka, domin su na amfani da layukan ne kawai don manufar su.

Kwamishinan ‘yan sandan, ya ce hukumar za ta ɗauki matakin kamawa tare da gurfanar da masu aikata waɗannan laifuffuka.

Leave a Reply