Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Yi Ma Wasu ‘Yan Mata Fyade A Jihar Kwara

‘Yan Bindiga Sun Yi Ma Wasu ‘Yan Mata Fyade A Jihar Kwara

138
0

Rundunar tsaro ta Civil Deffence reshen jihar Kwara, ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Nuku da ke karamar hukumar Kaiama.

Mai magana da yawun rundunar Babawale Afolabi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya na mai cewa sun shiga gidan wani Alhaji Hassan Yunusa, inda su ka sassare shi tare da wani dan’uwansa Woru Yunusa da adduna, sannan su ka yi awon gaba da ‘ya’yan sa mata kanana biyu zuwa cikin daji.

Babawale Afolabi, ya ce daga bisani Maharan sun sako yaran, amma sai da su ka yi masu fyade.

Ya ce sakamakon binciken da su ka gudanar ya nuna cewa, maharan sun shiga kauyen don su yi fashin kudaden mutane, amma da ba su samu ba sai suka tafi da ‘yan matan su ka aikata abin da su ka ga dama da su.

Afolabi, ya ce tuni likitoci sun dukufa duba lafiyar ‘yan matan, kuma rundunar ta fara gudanar da bincike domin kamo ‘yan bindigar.

Leave a Reply