Home Home Yan Bindiga Sun Sake Kashe Lauya A Zamfara

Yan Bindiga Sun Sake Kashe Lauya A Zamfara

97
0

‘Yan bindiga sun kashe wani lauya mai suna Barista Ahmad Muhammad Abubakar a Jihar Zamfara.

Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun bi margayin ne har gidan sa da ke garin Kwatarkoshi da ke Ƙaramar Hukumar Bungudu su ka hallaka shi.

Kafin rasuwar sa, marigayin ya rike mukamin sakataren walwala na Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya reshen jihar Zamfara, kuma shi ne ɗan takarar Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara na mazaɓar Bunguɗu ta Yamma a ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP a zaɓen da ya gabata.

Duk da dai Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Zamfara ba ta ce komai a kan batun ba, amma majiya ta kusa da marigayin ta tabbatar da faruwar lamarin manema labarai.

Wani mai suna Aminu Lawal Bungudu, ya ce bayan ‘yan bindigar sun shiga gidan marigayin ne su ka haɗu da matar sa lokacin da ta ke ƙoƙarin shiga ban-ɗaki, nan take su ka farmake ta amma ta saka ihun neman taimako mijin ta ya fito, daga nan ne su ka tafi da shi, inda a hanya su ka kashe su ka bar shi kwance cikin jini.

Leave a Reply