Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai 5 Da Malami Da Masu Gadi 2...

‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai 5 Da Malami Da Masu Gadi 2 A Neja

734
0
‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai 5 Da Malami Da Masu Gadi 2 A Neja
‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai 5 Da Malami Da Masu Gadi 2 A Neja

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai mata biyar da malami daya da kuma masu gadi a makarantar Tular Academy da ke karamar hukumar Mariga a jihar Neja.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Usman ya bayyana haka a lokacin da jami’an ‘yan sanda da sojoji su ka ziyarci makarantar jim kadan bayan aukuwar lamarin.

Haka kuma, kwamishinan ya ce ziyarar da rundunar ‘yan sandan suka kai makarantar, na daya daga cikin hanyoyin sanin salon tsaro da za a samar a makarantar.

Usman ya cigaba da cewa, tuni rundunar ta tura jami’an ta na musamman masu yaki da fashi da garkuwa da mutane a yankunan da lamarin ya faru domin ceto wadanda aka sace.

Kwamishinan ya bayyana yadda ‘yan bindigar suka yi amfani da matsalar sadarwa a yankin su ka sace daliban n makarantar, tare da daura laifin a kan karancin tsaro da makarantar ke fama da shi.

Usman ya kara da cewa, babu wani matsi da zai sa rundunar ta kasa sauke nauyin da ke kan ta na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar, sannan ya yi kira ga mutanan yankin su gaggauta kai rahoton duk wani al’amarin da ba su gane take-taken sa ba ga hukumomin tsaro mafi kusa da su.