Home Home ’YAN BINDIGA SUN KONE MUTUM 12 DA RANSU A KADUNA

’YAN BINDIGA SUN KONE MUTUM 12 DA RANSU A KADUNA

100
0

’Yan bindiga sun kona mutane 12 da ransu a kauyen Gindin Dutse Makyali da Doka da ke gundumar Kufana a karamar hukumar kajuru ta jihar Kaduna.

Haka kuma, ‘yan bindigar sun kona gidaje 17 a lokacin da suka kai hari a kauyen a safiyar ranar Lahadin da ta gabata.

Wani mazaunin yankin mai suna Stephen Maikori, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun jikkata wasu Karin mutane bakwai.

Jihar Kaduna dai, na ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan bindiga, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da lalata dukiya mai dumbin yawa.

Gwamnan Kaduna Uba Sani ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin, sannan ya yi Allah-wadai da kai harin, sannan ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA da ta tallafa wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su.

Uba sani ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa sa na magance matsalolin tsaron da Kaduna ke fuskanta, a wani makaki na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummar jihar

Leave a Reply