Wasu ‘yan bindiga sun kashe Arɗon Birni da Kewaye na
Masarautar Zazzau Alhaji Shuaibu Mohammed tare da wasu
‘ya’yan sa huɗu.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata da daddare, a ƙauyen Dorayi da ke Ƙaramar Hukumar Zaria.
Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar kimanin su biyar, sun kuma yi awon gaba da shanu 100 mallakar basaraken.
Matar marigayin Malama Halima Shuaibu ta shaida wa manema labarai cewa, maharan sun harbi magidan ta ne da bindiga a kai, lamarin da ya yi sanadiyyar ajalinsa nan take.
Ta ce ‘yan bindigar sun shiga ɗaki-ɗaki a gidan, inda su ka kashe ‘ya’yan ta huɗu masu aure har da ‘ya’ya.
Wani ɗan Arɗon da ya tsira da ransa, Abdurrahman Shuaibu, ya ce maharan sun kuma kashe wasu mutane biyu a hanyar su ta ficewa daga ƙauyen.