Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Jami’a A Katsina

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Jami’a A Katsina

32
0
43723b427bcc2b2392cf259309420c86
43723b427bcc2b2392cf259309420c86

‘Yan bindiga sun hallaka wani malami a jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma dake jihar Katsina.

An hallaka Dr. Tiri Gyan ne a sabon harin da ‘yan bindigar suka kai da sanyin safiyar yau Talata.

shaidan gani da ido ya shaida ta wayar tarho cewar, al’amarin ya faru ne da misalin karfe 1 da rabi na dare a gidan sa dake karamar hukumar Dutsin-Ma.

Ya kara da cewar ‘yan bindigar sun mamaye unguwar da muggan makamai,

suna harbin kan mai uwa da wabi, kana daga bisani suka yi awon gaba da 2 daga cikin ‘ya’yan malamin jami’ar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da afkuwar lamarin saidai yace nan bada jimawa ba rundunar zata fitar da cikakken bayani akai.

Dutsin-ma na cikin kananan hukumomi 10 dake fama da hare-haren ‘yan bindiga kusan a kowace rana duk kuwa da kokarin gwamnatin Katsina da hukumomin tsaro.

Leave a Reply