Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Arce Da Shugaban Ƙaramar Hukuma, Sun Bindige Dogarin Sa

‘Yan Bindiga Sun Arce Da Shugaban Ƙaramar Hukuma, Sun Bindige Dogarin Sa

154
0

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da Shugaban Ƙaramar
Hukumar Takum ta jihar Taraba Boyi Manga, sannan su ka
harbe ɗan sandan da ke tsaron lafiyar sa su ka kuma arce da
bindigar sa.

Wata majiya ta ce, an tare Boyi Manga ne tsakanin hanyarVChanchangi kusa da ƙauyen Agaraga da ke cikin Ƙaramar Hukumar Takum.

Majiyar ‘yan sanda ta ce, an yi garkuwa da Boyi Manga tare da kashe ɗan sanda mai tsaron lafiyar sa ne lokacin da su ke kan hanyar zuwa helkwatar Ƙaramar Hukuma.

Kakakin Yaɗa Labara na rundunar ‘yan Sanda ta Jihar Taraba Usman Abdullahi ya ce shi ma ya ji labarin, amma har yanzu ba a kai ma shi rahoto a kan lamarin ba.

Leave a Reply