Hukumomin ƙasar Poland, sun sako ‘yan Nijeriya 13 daga cikin 19 da ke tsare a sansanonin tsare ‘yan gudun hijira na ƙasar, bayan yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine ya kore su.
Hukumar kula da ‘yan Nijeriya Mazauna Ƙasashen Waje, ta ce
an sako mutanen ne bayan sa hannun da jakadan Nijeriya a
Poland Manjo Janar Christian Ugwu ya yi.
An dai kama mtanen ne bayan sun ƙi yarda su dawo Nijeriya,
lokacin da gwamnati ta ɗauki nauyin kwaso su daga ƙasashen
Poland da Romania da Hungary.
A cewar jakadan, ɗaya daga cikin mutane shidan da su ka rage a
hannun hukuma ya ce shi ɗan Kamaru ne, saboda mahaifiyar sa
‘yar can ce, amma sauran sun nemi mafaka daga gwamnati,
kuma ba za a sake su ba har sai gwamnatin Poland ta yanke
shawara a kan buƙatar su ta amincewa ko kuma watsi da ita.