Shugabar hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ketare Abike Dabiri-Erewa, ta ce akwai ‘yan asalin Nijeriya akalla miliyan uku da ke zama a kasar Sudan, kuma gwamnati ta na fadi-tashin kwaso duk wadanda yakin ya rutsa da su zuwa gida.
Abike, ta ce ana sa ran fara kwaso ‘yan ijeriya da yakin ya rutsa da su, bayan samun sahalewar bangarorin sojin da ke yaki da juna a Sudan.
Daga cikin ‘yan Nijeriya mazauna Sudan dai akwai dalibai akalla dubu biyar, wadanda su ka bayyana matukar kaduwa bayan barkewar yakin da ya haddasa rashin ruwan sha da abinci da kudi da layin sadarwa a birnin Khartoum. A baya-bayan nan ne rikici ya kara rincabewa a Sudan, tsakanin bangaren gwamnatin rikon kwarya ta kasar da mayakan RSF a kan shugabanci