Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yaki Da Ta’Addanci: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 46 a Jihar Zamfara

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta ce ta yi nasarar kama masu fashi da kisa da kuma satar mutane 46 tare da hallaka wasu 10 a jihar Zamfara.

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu, ya ce yayin aikin raba jihar da sauran makwaftan ta daga ‘yan ta’addar da su ka fara a makon jiya, sun kuma yi nasarar kubutar da wasu mutane biyu da aka sace.

Muhammad Adamu ya bayyana hakan ne, yayin wani taro da ya yi da kwamishinonin ‘yan sanda na jihohi a Abuja.

Da ya ke bayyana nasarar da ya ce sun yi a jihar Zamfara, wasu mazauna kauyukan Maikuru da Masha-awo a yankin Birnin-magaji, sun ce ‘yan bindiga sun afka wa kauyukan biyu, inda su ka kashe akalla mutane 32 tare da yin ta’adi a cikin kwanaki biyun da su ka gabata.

Exit mobile version