Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Sojojin Sama Sun Yi Luguden Wuta A Kan ‘Yan...

Yaki Da Ta’addanci: Sojojin Sama Sun Yi Luguden Wuta A Kan ‘Yan Ta’adda

720
0

Shelkwatar rundunar sojojin sama ta Najeriya, ta ce jiragen ta sun kai farmaki tare da rugurguza daya daga cikin manyan sansanonin ‘yan ta’addan ISWAP a yankin tafkin Chadi.

Mai magana da yawun shelkwatar ya ce, sun yi nasara a wani luguden wuta da su ka yi ta sama a yankin, bayan jirage masu leken asiri sun tattaro masu mahimman bayanai, nan take su ka dauki jiragen yaki tare da kai hari kan ‘yan ta’addan.

Ya ce sun lalata kayan amfanin ‘yan ta’addan da na’urar su ta wutar lantarki da sauran su.