Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Sojoji Sun Kubutar Da Mutane 8 Da Ke Hannun...

Yaki Da Ta’addanci: Sojoji Sun Kubutar Da Mutane 8 Da Ke Hannun ‘Yan Boko Haram

1049
0

Dakarun Sojin Nijeriya sun yi wa mayakan kungiyar Boko Haram kwantan bauna tare da kwato wasu mutane takwas da ke hannun ‘yan ta’addan.

Dakarun bataliya ta 121 tare da hadin gwiwar mafarauta ne suka samu wannan nasara a kauyen Gwadala, inda suka yi wa mayakan Boko Haram luguden wuta tare da kashe mutun guda daga cikin su da kuma jikkata wasu da dama.

Dakarun sojin dai, sun samu nasarar ceto wasu mutane Takwas da kungiyar ke rike da su, daga cikin su akwai mata biyu da yara kananan shida.

Kwamandan rundunar Birgediya Janar Abdulmalik Bulama Biu ya ce sabon salon yakin da rundunar ta kirkiro na kakkabe ragowa ‘yan ta’adda na taimakawa wajen samar da sakamako mai kyau musamman tun bayan kaddamar rundunar Operation Halaka dodo.

Janar Bulama Biu ya jinjina wa dakarun sojin da ke gudanar da aikin kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso gabas, inda ya kara da cewa, babban hafsan sojin kasa janar Tukur Yusuf Buratai ya yaba da aikin dakarun.

Leave a Reply