Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yaki Da Ta’Addanci: Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’Adda 12 A Sambisa

Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka ‘yan ta’addan Boko Haram 12 a dajin Sambisa da ke Jihar Borno, da kuma wasu mahara a Zamfara da Katsina.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar a nan Abuja.

Manjo Janar Nwachukwu ya ce sojojin sun yi galaba a kan ‘yan ta’addan a dajin Sambisa, inda suka kashe guda takwas a wani artabu da suka yi.

Ya ce a yayin farmakin, an yi kazamin artabu a tsakanin su wanda ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda, sannan sauran suka tsere.

A cewar sa, sojojin sun kwato bindigogi guda biyar, babura biyu da kuma kayan abinci da dama daga hannun ‘yan ta’addan.

Nwachukwu ya ce a wani samame da sojoji suka kai Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina, sun kashe ’yan ta’adda biyu, kazalika, ya ce sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku, da harsashi guda 57 da kuma sauran makamai.

Ya kara da cewa sojojin sun kuma ceto wani mutum, tare da kone baburan ’yan ta’addan guda biyu da kuma kone sansanin su a karamar hukumar.

Exit mobile version