Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yaki Da Ta’addanci: Janar Buratai Ya Ziyarci Dakarun Soji A Jihar Zamfara

A ranar Talatar da ta gabata ne, shugaban sojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya kai wa dakaru ziyara a sansanin ‘Hadarin Daji’ da ke birnin Gusau na jihar Zamfara domin kara masu karsashi da kwarin gwiwa.

Ziyarar Buratai dai ta na zuwa ne a daidai ranar da shugaban hafsin sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar ya hori dakaru a kan tabbatar da ganin karshen duk wasu masu tada zaune tsaye a fadin Nijeriya.

Kakakin rundunar sojin Nijeriya Kanar Sagir Musa, ya ce Buratai ya yi tattaki zuwa jihar Zamfara domin taya sojoji murnar bikin karamar Sallah, yayin da su ke filin daga na yakar ‘yan ta’adda.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kanar Musa ya ce Manjo Janar Lamidi Adeosun ne ya wakilci Janar Buratai wajen kai wannan ziyarar, inda ya hori sojoji a kan kawar da fargaba daga zukatan al’umma yayin kare martabar Nijeriya.

Exit mobile version