Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: An Kubutar Da Daliban Makarantar Kayar Maradun A Zamfara

Yaki Da Ta’addanci: An Kubutar Da Daliban Makarantar Kayar Maradun A Zamfara

188
0

Rahotanni daga jihar Zamfara sun tabbatar da cewa an kubutar da daliban makarantar sakandaren ‘Kayar Maradun da aka sace kwanaki.

A wani bidiyo da manema labarai ta samu daga jami’an jihar ta Zamfara, an ga Gwamna Bello Matawalle yana magana da wasu dalibai mata daga cikin wadanda aka kubutar din, yana tambayar su yanayin da suka samu kansu a hannun ‘yan bindigar.

Duk da rashin sadarwa da intanet da ake fama da aka katse su a jihar, a wani mataki na yakar ‘yan bindigar, wani jami’in gwamnatin Zamfaran da ya aiko wa bidiyon ya ce tun jiya Lahadi da marece aka kubutar da yaran.

Ya kara da cewa sai da jami’an suka je jihar Sokoto mai makwabtaka sannan suka iya aikawa da bidiyon.

Hukumomin sun ce an tarbi daliban ne a ranar Lahadi da yamma a fadar gwamnatin jihar, amma ba su bayyana yadda aka yi aka kubutar da su ba, walau ta hanyar biyan kudin fansa ne ko ta hanyar sasanci.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 1 ga watan Satumban nan ne ‘yan bindiga suka kai hari makarantar ta maza da mata da ke karamar hukumar Maradun kuma suka sace dalibai da dama.

Leave a Reply