Gwamnatin tarayya ta ce babban kalubalen da take fuskanta a yakin da take yi da kungiyar Boko Haram, shine karancin jami’ai a hukumomin tsaron Najeriya.
Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels, inda ya ce karancin jami’an tsaro ya sa ba a kowane gari ko kauye ake samun jami’an tsaron ba.
Garba, ya ce babban matsalar ita ce ba’a samun jami’an tsaro na tsawon sa’o’i 24 a kauyuka ko garuruwa, wannan kuma ya samo asali ne daga karancin adadinsu.
Garba, ya yaba tare da jinjinawa dakarun rundunar sojojin hadin gwaiwa dake yaki da Boko Haram a jihar Borno, inda ya ce suna matukar kokari, kuma aikin su na kyau. Malam Garba, ya koka kan karancin kudade a yakin da Sojoji ke yi da Boko Haram, amma ya daura laifi kacokan akan majalisar dokokin Najeriya, inda ya ce ta yi biris da bukatar shugaban kasa na diban dala biliyan daya daga asusun rarar man fetir domin sayen makamai.
You must log in to post a comment.