Hukumar yaki da almundahana ta jihar Kano ta bayyana cewa za ta binciki yadda ake biyan ma’aikatan jihar albashi.
Shugaban Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce binciken ya zama dole saboda yadda wasu ma’aikata ke ganin ana tura masu kudade masu yawa akan albashin su.
Magaji Rimin Gado, ya ce suna zargin akwai wata makarkashiya dake gudana a wajen biyan ma’aikatan jihar, saboda haka akwai bukatar a binciki lamarin.
Ya ce hukumar ta gano akwai ma’aikatan jihar da ake biya kudade fiye da albashinsu, kuma hukumar ta sami labarin cewa wasu ma’aikatan ma’aikatu da hukumomin gwamnati na ansar karin kudi fiye da albashin su.
Daga karshe ya yi kira ga ‘yan Najeriya su ba hukumomin hana cin hanci da rashawa goyan baya domin magance annobar cin hanci da rashawa.