Tsohon Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP Olisa Metuh, ya bayyana wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja aikin da ya yi da naira miliyan 400 da ya karba daga Gwamnatin Goodluck Jonathan.
Idan dai ba a manta ba, hukumar EFCC ce ta gurfanar da Metuh a kotu, inda ta nemi a hukunta, saboda kudin ba ta hanyar da ta dace ya karbe su ba.
A cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar EFCC Tony Orilade ya fitar, ya ce Olisa Metuh ya yi wa kotu bayanin yadda ya kashe kudaden da ya karba.
Olisa Metuh ya shaida wa kotun cewa, ya ki yi mata bayani ne tun farkon fara shari’a a shekarun baya, saboda kawai yadda EFCC ke ta babatu a kafafen yada labarai cewa ya danne naira miliyan 400.
Sai dai ya musanta zargin cewa ya ba wani dan canji mai suna Kabiru Ibrahim dala miliyan daya domin ya canja ko kuma a matsayin jarin da ya zuba a kamfanin sa.
You must log in to post a comment.