Majalisar wakilai ta bayyana kudurin ta na ganin bayan cin-hanci da rashawa ta hanyar sake karfafa hukumomin EFCC da ICPC, inda ta ce dokar da hukumomin ke aiki da ita a yanzu ta gaza wajen kawar da rashawa a Nijeriya.
Ta ce dokar hukumomin yaki da cin-hanci Nijeriya sun gaza kwarai da gaske, lamarin da ya sanya har yau an kasa magance matsalar rashawa da cin-hanci da ta zama ruwan dare a Nijeriya.
An dai fitar da wannan kuduri ne a zaman majalisar na ranar Alhamis da ta gabata, inda aka ambaci sabbin dokoki da tsare-tsaren musamman da za a iya amfani da su domin magance matsalar cin-hanci a Nijeriya.
Dan majalisa Julius Ihonvbare ne ya karanto kudurin, wanda bayan an tafka muhawara ya samu amincewar akasarin ‘yan majalisar wakilai.
Da ya ke jawabi game da shekaru ashirin na kafuwar dimokradiyya a Nijeriya, shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya ce ba su da wani abin da ke gaban su da ya wuce kare bukatun al’ummar su.