Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce za ta kashe Naira miliyan 288 a shekara ta 2019, wajen zuba wa injin janareto mai, da kudin sayen abinci, da kuma sayen jarida.
EFCC ta ce, kudin man janareto zai kai Naira miliyan 225, yayin da kudin sayen abinci zai kai naira miliyan 55, sanna kudin sayen jarida zai kai kimanin naira miliyan 7 da dubu 87.
Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya bayyana haka a Abuja, yayin da ya ke gabatar da kasafin hukumar na shekara ta 2019 a gaban kwamitin kasafi na majilisar tarayya a karkashin jagorancin dan majalisa Kayode Oladele.
Sai dai kudin da aka gabatar wa majalisar na hukumar ya ragu, inda ya ke nuna naira miliyan 111 a matsayin kudin man injin janareto, da naira miliyan 27 na abinci, da kuma naira miliyan 3 da dubu 87 a matsayin kudin jarida.
Ibrahim Magu, ya kuma nuna kudurin shi na kara wa ma’aikata 970 albashi da alawus.