Home Labaru Yaki Da Rashawa: EFCC Ta Sauya Salon Tuhumar Goje Bayan Ya Janye...

Yaki Da Rashawa: EFCC Ta Sauya Salon Tuhumar Goje Bayan Ya Janye Takarar Majalisa

379
0

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki  ta kasa wato EFCC ta janye tuhumar da take yi wa tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje, bayan janyewarsa daga takarar neman kujerar shugaban majalisar dattawa.

Lauyan da ke kare Goje, Wahab Shittu, ya shaidawa manema labarai cewar EFCC ba ta janye daga tuhumar da take yi wa Goje ba ne, kamar yadda kafafen yada labarai suka sanar da jama’a domin hukumar ba ta janye tuhuma a kansa ba.

Shittu ya ce ofishin ministan shari’a ne, bisa dogaro da karfin ikon da kundin tsarin mulki ya bashi, ya karbi ragamar tuhumar badakalar naira biliyan 25 da hukumar EFCC ke yi wa Goje.

 Ya ce hukumar EFCC ba ta da ikon kalubalantar karbar ragamar tuhumar Goje daga ofishin ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya.

Ministan shari’a, Abubakar Malami, ya karbi ragamar tuhumar Goje daga hannun hukumar EFCC,inda ta  shafe tsawon shekaru takwas tana tuhumar Goje da badakalar biliyan naira 25.