Hukumar yaki cin hanci da rashawa EFCC, ta sanar da kama wasu manyan jami’an gwamnati da na majalisar dokoki na jihar Kwara bisa harkallar biyan wasu ‘yan majalisu da na majalisar zartarwa kimanin naira miliyan 400 babu aikin fari balle na baki.
Kakakin hukumar EFCC Tony Orilade ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ofishin su da ke Ilorin ne ya fara gudanar da wannan bincike.
Sanarwar ta kara da cewa, EFCC ta fara binciken ne daga sakataren gwamnatin jihar Sola Gold, da akawun majalisar dokoki na jihar Jummai Kperogi, wadanda yanzu haka su na hannun hukumar, bisa zargin su da sa hannu wajen sakin kudaden ba tare da bin ka’idojin aiki ba.
Tony Orilade, ya ce sun samu korafin cewa, ‘yan majalisun dokoki 25 da wasu kwamishinonin jihar sun karbi naira miliyan 400 a matsayin kudin sallama, duk kuwa da cewa ma’aikata na bin gwamnatin jihar bashin albashin watanni uku.Sai dai akawun majalisar Jummai Kperogi ta bayyana wa EFCC cewa, tabbas kowane dan majalisa ya samu kudin sallamar sa, amma da amincewar gwamnan jihar Abdulfatah Ahmed aka biya.