Home Labaru Yaki Da Fasa Kwabri: Hukumar Kwastam Ta Kama Mota Makare Da...

Yaki Da Fasa Kwabri: Hukumar Kwastam Ta Kama Mota Makare Da Katan 600 Na Kodin

365
0

Hukumar yaki da masu fasa kwabri a jihar Legas, ta kama wata babbar motar dakon kaya makare da sinadarin kodin da kudin ta ya kai naira milliyan 240.

Shugaban hukumar a yankin Aliyu Mohammed, ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake nuna kayayyakin da aka kama a iyakar Najeriya.

Mohammed ya kara da cewa babbar motar na dauke da katan 600 na sinadarin kodin, kuma an kama ta ne a yankin Mile 2 da ke babban titin jihar Legas.

Shugaban hukumar ya ce direban motar ya gudu bayan ya hango tawagar jami’an hukumar a lokacin da suke gudanar da aikin sintiri domin farautar masu safarar miyagun kwayoyi.

Mohammed, ya kara da cewa a tsakanin watan Fabrairu zuwa Maris, shiyyar Legas ta kama katon na kwayoyin turamol dubu 1000 da buhun shinkafa dubu 13 da dari 810 da kuma wasu kwayoyi da kudinsu ya kai naira miliyan 105 da dubu dari 6.