Home Coronavirus Yaki Da Covid-19 Ganduje Ya Kaddamar Da Rabon Takunkumi Miliyan 2

Yaki Da Covid-19 Ganduje Ya Kaddamar Da Rabon Takunkumi Miliyan 2

234
0
Yaki Da Covid-19 Ganduje Ya Kaddamar Da Rabon Takunkumi Miliyan 2
Yaki Da Covid-19 Ganduje Ya Kaddamar Da Rabon Takunkumi Miliyan 2

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da rabon takunkumin rufe baki da hanci domin dakile yaduwar cutar COVID-19 a jihar.

Mai taimakawa gwamnan a kan harkokin yada labarai Salihu Tanko Yakasai ya bayyana haka a shafin sa na Facebook, tare da cewa adadin takunkumin ya kai miliyan 2, wanda aka samar bisa hadin gwiwar kananan hukumomin jihar 44.

Gwamna Ganduje ya ce, gwamnatin jihar ta samar da takunkumi guda miliyan guda, yayin da gamayyar kananen hukumomin jihar 44 suka samar da miliyan daya.

gwamnatin jihar Kano dai, ta wajabta sanya takunkumin rufe hanci da baki da daukacin al’ummar jihar domin a samu damar shawo kan annobar COVID-19.

Yanzu haka dai, jihar Kano na da mutane 666 da suka kamu da cutar Coronavirus.