Home Coronavirus Yaki Da Covid-19: Buhari Ya Gudanar Da Taro Da Kungiyar Gwamnonin Nijeriya

Yaki Da Covid-19: Buhari Ya Gudanar Da Taro Da Kungiyar Gwamnonin Nijeriya

389
0
Yaki Da Covid-19: Buhari Ya Gudanar Da Taro Da Kungiyar Gwamnonin Nijeriya
Yaki Da Covid-19: Buhari Ya Gudanar Da Taro Da Kungiyar Gwamnonin Nijeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da kungiyar gwamnonin Nijeriya domin tattaunawa a kan matsayar kwamitin yaki da cutar Coronavirus da ya kafa.

Tattaunawar dai, ta gudana ne ta hanyar yanar gizo karkashin jagorancin shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, inda Buhari ya kuma umarci kwamitin yaki da cutar ya yi aiki tare gwamnonin jihohi domin samun damar shawo kan annobar covid-19 a fadin Nijeriya.

Shugaban kasa Buhari ya jaddada cewa, akwai bukatar ilimantarwa tare da wayar da jama’a domin su fahimci illolin cutar da hanyoyin dakile yaduwar ta.

Buhari ya kara da cewa,  yin aikin kafada da kafada da kwamitin yaki da cutar Coronavirus da kuma daukacin gwamnonin Nijeriya  zai matukar taimakwa wajen rage yaduwar annobar.