Home Labaru Yaki Da Boko Haram: Za Mu Fatattaki Sojojin Da Ba Su Tabuka...

Yaki Da Boko Haram: Za Mu Fatattaki Sojojin Da Ba Su Tabuka Komai – Buratai

313
0

Shugaban hafsan sojin Nijeriya Laftanal Janar Tukur Buratai, ya yi gargadin cewa rundunar soji a karkashin ikon sa za ta tsamo sojojin da ba su da niyyar tabuka komai a fagen yaki da mayakan kungiyar Boko Haram.

Da ya ke bayyana iri wadannan sojojin a matsayin bara-gurbi, Buratai ya ce yunkurin sa na son kawo sauyi ba zai jira irin wadannan sojoji su bada hanya ba, maimakon haka zai fatattake su ne.

Kakakin rundunar sojin Nijeriya Kanal Sagir Musa, ya ce Buratai ya bayyana haka ne a helkwatar rundunar da ke Abuja, yayin da ya ke jawabin rufe wani taro na rundunar.

Kanar Musa ya ce, Janar Buratai ya bukaci jami’an rundunar su kasance masu alfahari da rawar ganin da su ke takawa, a kokarin su na kare martaba da mutuncin Nijeriya.