Home Home Yakar Miyagun Kwayoyi: Najeriya Ta Nemi Hadin Kan Kasashen Afirka

Yakar Miyagun Kwayoyi: Najeriya Ta Nemi Hadin Kan Kasashen Afirka

50
0

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA Manjo janar Buba Marwa mai ritaya, ya ce musayar bayanan sirri tare da karfafa hadin gwiwwa tsakanin kasashen Afirka zai taimaka wa kasashen nahiyar wajen yakar matsalar shaye-shaye da safarar miyagun kwayoyi.

Buba Marwa ya bayyana hakan ne ranar Laraba a wajen taron shugabannin hukumomin yaki da miyagun kwayoyi na nahiyar Afirka da ke gudana a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Yayin da yake jawabi game da nasarar da Najeriya ta samu wajen yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, Buba Marwa ya ce ana bukatar hadin kan kasashen nahiyar wajen samar da hanyoyin da za a yaki dabi’ar safarar muggan kwayoyi a fadin kasashen nahiyar.

Ya kara da cewa tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2022, NDLEA ta kama mutum 21,302 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi ciki har da manyan diloli 28.

Haka kuma ya ce hukumar tasa ta kama miyagun kwayoyin da nauyinsu ya kai kilogiram miliyan 5.4, tare da sauya wa fiye da mutum 12,326 masu amfani da kwayoyin tunani.