Shugaban kungiyar likitocin Najeriya Dr. Orji Emeka Innocent, ya ce yajin aikin da kungiyar likitocin Najeriya NARD ta fara ya jefa harkoki da cibiyoyin kiwon lafiyar jama’a a Najeriya cikin halin ha’ula’i.
Dr. Orji Emeka Innocent, ya ce ‘ya’yan kungiyar sun bi duk hanyoyin da suka dace a ƙoƙarin su na ganin an warware rikicin amma hakar su bata cimma ruwa ba.
Ya ce a asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke Kano, an umarci mutane su mayar da ‘yan uwan su marasa lafiya gida saboda babu likita da zai duba su, yayinda a Legas kuma likitoci na ci gaba da kula da majinyatan da aka kwantar da su amma ba su karban sabbin marasa lafiya.
A halin da ake ciki dai likitoci masu neman ƙwarewa wadanda ke da kaso mafi tsoka a manyan asibitocin gwamnati, sun ce sun shiga yajin aiki ne har sai gwamnati ta biya musu bukatun su na albashi da kudin walwala.