Home Labarai Yadda Wani Matashi Ya Yi Wa ‘Yar Makwabcin Sa Yankan Rago a...

Yadda Wani Matashi Ya Yi Wa ‘Yar Makwabcin Sa Yankan Rago a Jihar Kano

139
0

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano, ta tabbatar da kama wani matashi bisa zargin garkuwa da wata yarinya mai suna Zuwaira Gambo tare da yanka ta a garin Sabon Fegi da ke garin Tofa.

Ta ce ta samu gawar yarinyar mai shekaru 13 ne a wani kango
da ke garin Tofa kwana guda da ɓatan ta.

Rundunar ta ce ta kama matashin ne bayan sama da kwanaki
dari biyu da faruwar al’amarin, a lokacin da ya ke shirin karbar
kudin fansar kanin marigayiyar.

Mai magana da yawun rundundar ‘yan sanda na jihar Kano DSP
Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce matashin mai suna Auwwalu
Abdulrashid da ake yi wa laƙabi da Lauje, ya na makwaftaka ne
da gidan wadda ake zargin shi da kashewa.