Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yadda Shugabannin Duniya Ke Tururuwar Rantsar Da Tinubu

Gabanin bikin rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu, babbar hukumar Birtaniya da ke Abuja ta fitar da jadawalin wata tawaga da za ta halarci bikin.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar Dean Hurlock ya bayyana haka, inda ya ce tawagar za ta kasance a karkashin jagorancin Firayin minista Andrew Mitchell, da karamin Ministan Ci-Gaban Afirka a Ofishin Harkokin Waje, tare da Wakilin Firayin Ministan Harkokin Kasuwanci a Nijeriya da kuma Wakiliyar Musamman a kan Ilimin ‘Yara Mata Helen Grant, da Babban Kwamishinan Birtaniya a Nijeriya Dakta Richard Montgomery.

Yanzu haka dai, haifaffen Nijeriya Enoh Ebong ya na daga cikin tawagar wakilai tara da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar, wadan da za su halarci bikin rantsar da Bola Tinubu a Abuja.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar, ta ce tawagar za ta kasance a karkashin Sakatariyar Gidaje da Raya Birane ta Amurka Marcia L. Fudge.

Exit mobile version