Tsohon shugban kasa, Janar Yakubu Gowon ya ce shi da wasu manyan ‘yan Najeriya ne suka roki tsohon kakakin majalisar wakilai Ghali Umar Na’Abba da tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim kada su tsige Tsohon shugban kasa, Olusegun Obasanjo akan karagar mulki.
Karanta Labaru Masu Alaka: Farfesa Yemi Osinbajo Ya Zargi Manyan ‘Yan Siyasar Nijeriya
Gowon, ya bayyana hakan ne a a lokacin da yake jawabi a wajen da aka shirya na karrama marigayi Manjo Janar Emmanuel Olumuyiwa Abisoye a Abuja.

Tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya ce shi da Abdulsalami Abubakar da tsohon shugaban kasa Ernest Shonikan da wasu manyan ‘yan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wurin hana shugabanin majalisar tarayyar na wancan lokacin tsige Obasanjo.
Ya ce a lokacin da ” Ghali Na’Abbah ya na nan kuma ya tabbatar da cewa mun tattaunawa wasu batutuwa masu muhimmanci tare da roko kuma suka amince saboda suna ganin girman mu.
Karanta Labaru Masu Alaka: Osinbajo Ya Bayyana Hadin Kai A Matsayin Mafita Ga ‘Yan Nijeriya
Ya ce abinda ya hana su bari a tsige shugaban kasa shi ne, a lokacin dimokradiyya na jinjira, amma da sun bari an yi hakan, da babu wani shugaban kasa a Najeriya da hakan ba za ta iya furuwa da shi ba.
You must log in to post a comment.