Jami’an hukumar kwastam da ke aiki a wani shingen bincike a
karamar hukumar Garki ta jihar Jigawa,’a sun harbe wani
abokin aikin su da ke dawowa daga jamhuriyar Nijar bayan ya
ki tsayawa yi masa bincike.
Jami’an kwastam da ke aiki a shingen binciken dai sun shiga shakku lokacin da motar jami’in mai suna Muhammad Sayyadi ya nufo shingen, sannan ya ki tsayawa a bincike shi.
A cikin rashin sani, ashe jami’in ya na dawowa ne daga garin Magarya bayan ta’aziyyar da ya kai wa tsohon jakadan Nijeriya a Korea Ta Kudu Ali Magashi bisa rasuwar mahaifiyar sa.
Sai dai lamarin ya nemi tada hankalin mutanen yankin Ringimna, lokacin da su ka fahimci cewa Sayyadi dan Sarkin Ringim ne.














































