Home Labaru Yadda Ɗan Takarar Gwamna A PDP Ya Raba Katin ATM 200,000 A...

Yadda Ɗan Takarar Gwamna A PDP Ya Raba Katin ATM 200,000 A Ranar Zaɓe

103
0

Jigon jam’iyyar PDP Ladi Adebutu, ya shiga tsomomuwa
bayan ‘yan Sanda sun ce ya gudu daga Nijeriya ne saboda sun
bankaɗo wata gadangarƙamar da ya shirya ta sayen ƙuri’u da
naira biliyan 2 a lokacin zaɓen shekara ta 2023.

‘Yan sanda sun ce, Adebutu wanda ya yi takarar gwamnan jihar Ogun a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya yi watandar naira biliyan 2 domin sayen ƙiri’un masu zaɓe a ranar 18 Ga watan Maris.

Wannan zargin dai ya na daga cikin rahoton da ‘yan sandan bincike su ka gabatar wa shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya.

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Ogun Abdullahi Sanusi ne ya aika wa Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Ogun takardar ƙorafi, inda ya ce Adebutu ya riƙa raba katin ATM, wanda kowanne an loda ma shi Naira dubu 10 aka riƙa rabawa a ranar zaɓe.

Daga nan ne aka naɗa ‘yan sandan bincike a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Mohammed Babakura, wanda ke Ofishin Binciken Manyan Laifuffuka a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Leave a Reply